AFCON: Koulibaly ya mayar wa Napoli martani

Dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly da ya fice daga Napoli a cikin shekarar nan, ya soki matsayar mamallakin Napolin da ke son hana 'yan wasansa da ke da tushe da Afirka zuwa gasar AFCON.


Dan wasan baya a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Kalidou Koulibaly, ya yi kira ga mamallakin tsohon kulob dinsa na Napoli ta lig din Serie A na Italiya da ya mutunta kungiyoyin kwallon kafa na Afirka, a daidai lokacin da furucin jami'in na Napoli ke ci gaba da fusata 'yan kwallon kafar Afirka da ke Turai.


A ranar Talata ce dai aka ruwaito  Aurelio De Laurentiis na cewa daga yanzu ba zai sanya hannu a kwantaragi da wani dan kwallo na Afirka ba, har sai dan wasan ya amince a rubuce cewa ba zai shiga gasar kwallon kafar Afirka ta AFCON ba. Mai kulob din Napolin, ya ce ya lura a duk lokacin da aka zo gasar AFCON ba ya samun hankalin 'yan wasansa na Afirka. 

News Source:  DW (dw.com)