Aikin yara kanana na karuwa a duniya

Aikin yara kanana na karuwa a duniya
Asusun yara kanana na MDD UNICEF ya ce a karon farko cikin goman shekaru an samu karuwar aikace-aikace na yara kanana a duniya.

A farkon shekara ta 2020 kimanin yara miliyan 150 maza da mata suka tsunduma cikin aikin, abin da kungiyar ma'aikata ta duniya OIT ta ce aikin yara kananan ya karu da yara miliyan takwas da rabi a cikin shekaru hudu kawai. Shugabar asusun na UNICEF Henrieta Fore ta ce halin da duniya ta fada ciki na annobar corona ya kara assasa aikin na yara kanana. Asusun na UNICEF ya bayyana wannan rahoto ne a jajibirin ranar da MDD ta ware domin yaki da aikin yara kananan a ranar 12 ga wannan wata watau ranar

Asabar.
 

News Source:  DW (dw.com)