Amirka na fafutukar yaki da corona

Amirka na fafutukar yaki da corona
Amirka ta ce za ta saye alluran rigakafi na corona kimanin miliyan 500 domin rarraba su ga kasashe matalauta.

Amirkan ta ce ta cimma yarjejeniya da kamfanonin Pfizer da Biontec domin samar da alluran riga kafin. An hirya Shugaba Joe Biden zai bayyana ba da tallafin a wajen taron kasashe masu karfin tattalin arzikin masana'antu G7 da za a yi Cornwall a Birtaniya a ranar Juma'a(11-06-2021). Da farko kasashe 92 za su samu wannan tallafi wanda za a fara isar da shi a cikin watan Augusta.
 

News Source:  DW (dw.com)