Amirka za ta yi rigakafi ga wadanda suka balaga

Amirka za ta yi rigakafi ga wadanda suka balaga
Shugaban kasar Amirka Joe Biden ya sha alwashin samar da alurar rigakafin corona da za ta isa a yi wa daukacin mutanen kasar da shekarunsu suka haura sha takwas zuwa karshen watan mayun wannan shekarar.

Mista Biden ya kuma bukaci jihohin kasar da su yi kokarin samar da zagayen farko na rigakafin ga malaman makaranta zuwa karshen wannan wata na Maris da muke ciki domin hanzarta bude makarantun kasar da suka kwashe tsawon lokaci suna kulle a sabili da annobar.Haka zalika fadar White House ta sanar da kamfanin samar da magunguna na Merck zai taimaka wajen samar da karin wasu rigakafin da kamfanin Johnson & Johnson tuni ya fara samar wa.
 

News Source:  DW (dw.com)