Amnesty: Yara na kara shiga ta'addanci a Nijar

Amnesty: Yara na kara shiga ta'addanci a Nijar
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International, ta ce ana ci gaba da samun karuwar kananan yara da hare-haren ta'addanci ke samun su a Jamhuriyar Nijar.

Cikin wani rahoton da ta fitar a yau Litinin,Amnesty Internationalta kuma ce akwai yara kananan da dama da ake tilasta wa zama mayakan kungiyoyin masu tsattsaurar ra'ayi a iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso.

Sama da kananan yara 60 ne suka rasa rayukansu a yankin Tillaberi da ke na Nijar, daga farkon wannan shekara zuwa halin da ake ciki.

Rahoton kungiyar ya nuna cewa rayukan mutane 544 suka salwanta a fadin Nijar sakamakon hare-hare daga ranar daya ga watan Janairu zuwa 29 ga watan Yulin bana.

Rahoton dai na zuwa ne makonni biyu bayan wasu 'yan bindiga a bisa babura sun kashe mutane 11 a garin Garba Kouara a yankin Tillaberi.

News Source:  DW (dw.com)