Amurka: Mahawarar 'yan takara kan corona

Amurka: Mahawarar 'yan takara kan corona
Shugaban Amurka Donald Trump da abokin hamyyararsa na jam'iyyar Demokrats Joe Biden sun amsa tambayoyin alummar kasar kai tsaye a wani taron majalisar gari.

Dukkanin 'yan takarar biyu sun assasa hujjojinsu da suke ganin ya kamata a zabe su.

Batun annobar coronavirus shi ne ya fi mammaye taron, da aka tambayi Mr Trump a kan batun saka takunkumi kasancewar a baya an sha kai ruwa rana da shi game da batun, Mr Trump ya ce yana nan a kan bakar shi, duk da cewar yana goyon bayan sanya makarin, ya kuma kara da cewar kaso 85 cikin dari na wadanda suka kamu da cutar masu saka takunkumin ne.

A nashi bangaren madugun adawa Biden ya yi amfani da wannan dama wajen caccakar shugaban na Amurka a kan yadda ya ke wa lamarin cutar rikon sakainar kashi.
 

News Source:  DW (dw.com)