An kashe wani babban soja a Guinea

An kashe wani babban soja a Guinea
Hukumomi a Guinea sun ce 'yan bindiga sun hallaka wani Kanar na soja da ke jagorantar wata bataliyar dakaru na musamman a yayin da fargaba ke karuwa a kan zaben kasar.

Wasu 'yan bindiga dadi, sun bindige wani Kanar na soja a kasar Guinea Conakry, kwanaki biyu gabanin babban zaben da za a yi a kasar.

Hukumomi a kasar sun ce 'yan bindigar sun hallaka Kanar Mamady Conde, wanda ke jagorantar wata bataliyar horar da dakaru na musamman a Kindia, birni na hudu mafi girma a kasar.

'Yan kasar dai na shirin zaben ne cikin fargaba saboda ganin yadda takara za ta iya yin zafi tsakanin Shugaba Alpha Conde da madugun adawa Cellou Dalein Diallo.

An dai tabbatar da takarar Shugaba Alpha Conde ne bayan sauya kundin tsarin mulkin kasar da ya ba shi damar takara karo na uku.

Hakan kuwa ya sanya wasu bangarori cewa kasar ta bi sahun wasu shugabanni a Afirka da ke da manufar mulki na mahadi ka ture.

News Source:  DW (dw.com)