An kona daruruwan ofisoshin 'yan sanda a yayin rikicin ENDSARS

An kona daruruwan ofisoshin 'yan sanda a yayin rikicin ENDSARS
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce jami'ai akalla 25 ne suka rasa rayukansu wasu da dama yanzu haka ke jinya a asibiti a sakamakon rikicin da ya barke a yayin zanga-zangar ENDSARS na watan Oktoba.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar da sanarwa a wannan Juma'a kan ta'asar rikicin dandalin Lekki na jihar Legas. Mai magana da yawun rundunar Frank Mba, ya ce jami'anta akalla ashirin da biyu ne suka mutu a yayin da aka kona ofisoshin 'yan sanda kimanin dari biyu da hamsin, alkaluman na tsawon lokacin da aka kwashe ne ana zanga-zangar ENDSARS a cikin watan Oktoba a kasar.

Jami'in ya kara da cewa, akwai karin jami'an da suka ji rauni, wasunsu yanzu suna kwance a asibiti a cikin mawuyacin hali. Mista Mba, ya ce jami'an sun rasa rayukansu a yayin da suke kokarin tabbatar da zaman lafiya duk kuwa da barazanar da rayukansu ke ciki a lokacin boren.

Sai dai, bai ce komai ba, kan zargin jami'an da aka yi da laifin kisan masu zanga-zangar a yayin jawabin nasa. Amma rahotannin da suka yi ta karo da juna dai, sun zargi jami'an da soma bude wuta kan masu zanga-zangar, lamarin da aka ce, ya yi sanadiyar rayukan fararen hula sama da hamsin, batun da rundunar ta musanta.

News Source:  DW (dw.com)