An saki matukan jirgin ruwan Turkiyya

An saki matukan jirgin ruwan Turkiyya
Wani gidan talabijin na Turkiya a yau Juma'a, ya bayar da sanarwar sakin ma'aikatan jirgin ruwan nan da aka yi garkuwa da su a gabar ruwan Najeriya, bayan shafe makwanni biyu a hannun 'yan fashin teku.

Illahirin ma'aikatan jirgin dai 'yan asalin kasar Turkiyar ne, sai wani guda dan asalin kasar Azerbaijan wanda barayin suka hallaka.

Jirgin da ya nufi birnin Cape Town na Afirka ta Kudu, an sauya masa akala ne bayan tashinsa da kilomitoci 160 daga birnin Legas na Tarayar Najeriya.

Sai dai babu bayanan hanyoyin da aka bi wajen sakin ma'aikatan, an biya kuddaden fansa ko ko a'a.

News Source:  DW (dw.com)