An sako wasu daliban Kaduna a Najeriya

An sako wasu daliban Kaduna a Najeriya
A Najeriya, an sako dalibai 10 daga cikin 'yan makarantar Bethel Baptist High School ta Kaduna, wadanda masu garkuwa da mutane suka sace watanni biyu da suka gabata.

Shugaban makarantar Bethel Baptist High School ta Kaduna, Reverend John Hayab, wanda ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Reuters sakin daliban, ya ce har yanzu da sauran dalibai 21 da masu garkuwar ke rike da su.

Reverend Hayab, ya ce an biya kudin fansa kafin a kai ga sakin takwas daga cikin daliban, yayin kuma da aka saki biyu daga cikin su saboda yanayi rashin lafiya da suke ciki.

Ko a watan jiya ma dai, masu garkuwar sun sako yara 15 daga cikin daliban, bayan sakin wasu 28 cikin watan Yuli.

Kimanin daliban na Bethel Baptist 150 ne 'yan binduigar suka kwashe cikin watan na Yuli.

Reverend John Hayab, ya ce kudi ne suke nema ya sa suke sakin daliban rukuni-rukuni.

News Source:  DW (dw.com)