An tsaurara tsaro gabanin tsige Shugaba Trump

An tsaurara tsaro gabanin tsige Shugaba Trump
Wakilai a majalisar dokokin kasar Amrika na tafka turancin neman kawo karshen mulkin shugaban kasa, inda ake sauran kwanaki kalilan da karewar wa'adinsa a kan karaga.

Majalisar wakilan Amirka, ta shirya tsige Shugaba Donald Trump inda wakilai kuma kusoshi a jam'iyyar Republican da ke mulki masu yawa ke goyon bayan 'yan jam'iyyar Democrats masu adawa, a zaman da ake yi a wannan Laraba.

An dai baza dubban sojojin kundumbala wandanda ke zaman ko-ta-kwana a sassa daban-daban na birnin Washington, inda a wasu wuraren aka datse hanyoyin da aka saba zirga-zirga ta yau-da-kullum.

Shi dai Shugaba Donald Trump na cikin tsaka mai wuya ne, bayan tunzura magoya bayansa da ya yi a makon jiya, inda suka far wa majalisar dokokin kasar lokacin da ake tabbatar da zaben Joe Biden a matsayin zababben shugaban Amirkar.

Kuri'ar neman tsige shugaban a karo na biyu, na zuwa ne yayin da ake mako guda kafin karewar wa'adinsa a matsayin shugaban kasa.

News Source:  DW (dw.com)