An tsige shugaban kasar Albaniya

An tsige shugaban kasar Albaniya
Shekara guda gabanin kawo karshen wa'adin mulkinsa majalisar dokokin Albaniya a wani zaman da ta kira na musamman ta tsige shugaban kasar  Ilir Meta bisa dalillai na cewa shugaban ya taka dokokin kasa.

Firaministan kasar  Edi Rama a cikin jawabinsa gabanin fara kada kuri'ar a zauren majalisar ya tabbatar da cewa shugaba Meta ya saba wa kundin tsarin mulki ta hanyar taka dokokin zaben kasar yayin zabukan yan majalisa da aka gudanar a watan Apirilun da ya gabata.

Kotun kundin tsarin mulkin kasar ce kawai ke da hurumin tabbatar da tsigewar da aka yi wa shugaban cikin  watanni uku. Sai dai Mista Metan ta bakin mai magana da yawunsa Tedi Blushi ya bayyana tsigewar a matsayin wasan yara da ta saba doka.
 

News Source:  DW (dw.com)