Bajamushe ya karbi rigakafin corona sau 87

Bajamushe ya karbi rigakafin corona sau 87
Kungiyar Red Cross a Jamus na zargin mutumin da sayar wa da jama'a shaidar karbar rigakafin corona 87 da ya karba. Sai dai shi kuma bai kai ga bayyana dalilinsa na daukar wannan mataki ba.

Hukumomi a Jamus sun kama wani Bajamushe da ya yi rigakafin corona akalla sau 87. Rahotanni sun ce mutumin ya rika karbar rigakafi sau uku a kowace rana a cibiyoyin yin rigakafin dabam-dabam na jihar Saxony da ke gabashin Jamus. 


Asirin mutumin ya tonu bayan da wani malamin asibiti ya gane fuskarsa a matsayin wanda ya jima yana zuwa karbar rigakafi a wata cibiya, nan take ya kira 'yan sanda suka zo su kama mutumin da kawo yanzu ba a bayyana sunansa ba. 


Bajamushen dai ya rika gabatar wa malaman rigakafi, sabon katin shaidar rigakafi wanda ba ya nuna cewa an yi masa rigakafin corona a baya. Da zarar an kammala yi masa sai ya yage takardar ya sake nausawa wata cibiyar rigakafin domin cimma burinsa.

News Source:  DW (dw.com)