Bakin haure sun mutu a turmutsitsi

Bakin haure sun mutu a turmutsitsi
Bakin haure da suka fito daga kasashen Afirka akalla 18 ne suka mutu a yayin wani turmutsitsin tsallaka shinge don shiga kasar Spaniya.

Wasu bakin haure da suka fito daga sassa dabam-dabam na Afirka guda goma sha takwas, aka tabbatar sun mutu a yayin wani turmutsitsin tsallaka shinge da ya raba kasar Moroko da kasar Spaniya a ranar Juma'ar da ta gabata.

Bakin haure sama da dubu biyu ne suka yi yunkurin haura katangar shingen, wasu sun fado daga saman shingen da ya raba kasashen biyu, akwai  jami'an tsaro kimanin dari da arba'in da kuma bakin haure saba'in da shida da suka ji rauni a yayin yunkurin tsallakawa. 

An kafa katangar a mashigin tekun na Melilla na kasar Spaniya, don hana bakin haure tuttudowa Turai daga Moroko, sai dai ya kasance tamkar tarkon mutuwa ganin yadda ake ci gaba da tafka asarar rayuka a saboda yadda bakin haure ke kasadar shiga Turan duk da barazanar rasa rai.
 

News Source:  DW (dw.com)