Barazanar gwajin makaman nukiliya

Barazanar gwajin makaman nukiliya
Wani binciken sirri na Majalisar Dinkin Duniya ya gano sabon shirin Koriya ta Arewa na kera makaman nukiliya da duniya ke wa kallon mai hadarin gaske.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ta gano wani sabon shirin Koriya ta Arewa na soma gwajin makaman nukiliya. A binciken sirri da ta ce ta gudanar, an gano yadda Pyongyang ta soma wasu aikace-aikacen kera makaman masu hadari a wani kebabben wuri da ke a yankin arewacin kasar.  Rahoton ya kuma yi gargadin karuwar samar da sinadarin Uranium da aka inganta a wasu wurare a Koriya ta Arewa.  

Kasashen duniya da dama, sun sha danganta gwajin makaman nukiliyan da Koriya ta Arewa ke yi a matsayin babbar barazana. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakkausar suka da kuma barazanar daukar mataki. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Chaina ta soma harba wasu makamai masu linzami a cikin tekun da ke kusa da makwabciyarta Taiwan dama yi wa tsibirin kawanya, bayan da ta fusata da ziyarar Shugabar Majalisar Wakilan kasar Amirka Nancy Pelosi a Taiwan din. 

News Source:  DW (dw.com)