Belarus: Lukashenko ya gargadi kungiyar EU

Belarus: Lukashenko ya gargadi kungiyar EU
Shugaban Belarus Alexander Lukashenko ya yi barazanar mayar da martani idan wata kasa ta kuskura ta sanya wa kasarsa takunkumi.

Shugaba Alexander Lukashenko na Belarus ya ce zai hada karfi da sojojin kasar Rasha domin tunkarar barazanar da kasashen yammacin duniya ke masa.

Kurarin na Lukashenko na wannan Jumma'a na zuwa ne a yayin da kungiyar tarayyar Turai ta sanar da cewa ta tsara wasu takunkumai da za ta kakaba wa kasar ta Belarus bisa yadda Shugaba Lukashenko ke dirar mikiya a kan masu adawa da sake zabarsa a kasar. 

Tun daga ranar 9 ga watan nan na Agusta ne dai jama'ar Belarus ke zanga-zangar nasarar da aka bai wa Lukashenko a zaben kasar, yayin da shugaban ke amfani da jami'an tsaro wurin tarwatsa su.

News Source:  DW (dw.com)