Binciken irin ta'asar da ake tabkawa na karbar rashawa

Binciken irin ta'asar da ake tabkawa na karbar rashawa
Transperancy International ta bayyana Amurka da Birtaniya a matsayin wadanda suka fi kowace kasa fitar da kaya zuwa ketare da jajircewa wajen kafa dokokin da ke da nufin haramtawa kamfanoni biyan kudaden cin hanci.

Kungiyar yaki da rashawa ta kasa da kasa ta Transperancy International, ta bayyana kasashen Amurka da Birtaniya a matsayin wadanda suka fi kowace kasa fitar da kaya zuwa ketare da jajircewa wajen kafa dokokin da ke da nufin haramtawa kamfanoni biyan kudaden cin hanci a kasuwannin ketare. Sai dai kungiyar ta ce wasu kasashen basa tabuka komai a wannan bangare.

Kungiyar ta Tranparency mai matsuguni a birnin Berlin na tarayyar Jamus, ta kara da cewa a shekara ta 2019, kasashe hudu ne kacal da suka hadar da Amurka da Birtaniya da Switzerland da Izra'ila daga cikin 47, da ke wakiltar kashi 16.5 na yawan kayan da ake fitarwa zuwa ketare, suka taka rawa wajen aiwatar  dokar haramta bayar da cin hanci.

Hakan na nuna koma baya game da rahoton kungiyar a shekara ta 2018, lokacin da ta ayyana kasashe bakwai da ke wakiltar kaso 27 daga cikin 100 na masu fitar da haja zuwa ketare da aiwatar da dokar. A cewar jagoran marubuta rahoton na wannan shekarar Gillian Dell dai, kasashe da dama basa binciken irin ta'asar da ake tabkawa na karbar rashawa a ketare.
 

News Source:  DW (dw.com)