Chaina na shirin harba wa Taiwan makamai

Chaina na shirin harba wa Taiwan makamai
Kungiyar Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da matakin da Chaina ke dauka. Amma Rasha ta goyi bayan Chaina tare da zargin Amirka da kokarin fusata Beijing don daukar mataki irin wanda ita Rashan ta dauka a kan Ukraine.

Hukumomin Chaina sun kaddamar da gagarumin atisayen soji a ranar Alhamis a nisan kilomita 20 da kasar Taiwan, kuma Beijing na shirin harba makamai masu linzami da ka iya gittawa ta tsuburin. Sai dai hukumomin Taiwan suka ce za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin kare kansu daga abin da suka kira taba martabarsu ta zama kasa mai cikakken iko daga abokan gaba ba.

Hakan dai ta biyo bayan ziyarar kakakin majalisar wakilan Amirka, Nancy Pelosi, da ta kai wa Taiwan a ranar Laraba duk da gargadi da Chaina ta yi cewa idan har 'yar siyasar ta Amirka ta ziyarci Taiwan din, za ta dauki mataki. 

Chaina dai ta jima tana daukar Taiwan a matsayin bangaren kasarta da ya fandare. Sai dai hukumomin Taiwan sun sha nuna kansu a matsayin kasa mai cikakken iko. 

 

News Source:  DW (dw.com)