COVID 19 ta assasa yunwa a duniya

COVID 19 ta assasa yunwa a duniya
MDD ta ce a bara an samu karin mutanen da ke fama da yunwa da wajen miliyan 10, tare da gargadin cewar annobar coronavirus na iya kara yawansu zuwa miliyan 130 a 2020.

Wannan adadi na kunshe ne cikin rahoton baya-bayannan na hukumar kula da samar da abinci mai gina jiki ta duniya, da ke cikin rahoton shekara-shekara na hukumomin MDD guda biyar wadda aka wallafa a wannan Litinin.

Wannan hasashen na nuni da cewar, annobar ta COVID-19 na iya kara yawan mutane miliyan 83 a kan miliyan 132 da ke da akwai cikin rukunin wadanda ke fama da karancin abinci mai gina jiki.

A cewar mawallafa rahoton dai, matsalar farin dango da aka fuskanta a yankin gabashin Afirka na iya assasa halin yunwa da za a fuskanta a wannan shekarar.

News Source:  www.dw.com