Cutar corona na karuwa a nahiyar Turai

Cutar corona na karuwa a nahiyar Turai
Nahiyar Turai ta haura dubu dari da hamsin na yawan sabbin kamuwa da cutar corona a cikin sa'o'i 24, mako guda bayan sanar da samun mutum dubu dari a karon farko. 

Alkaluman kididiga sun nuna kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya sune suka fi samun karuwar cutar a wannan makon.

Yanzu haka Turai na samun yawan masu kamuwa da cutar fiya da kasashen Indiya da Brazil da kuma Amirka. 

A karon farko tun bayan bullar cutar, gabaki daya a fadin duniya an sami mutane sama da dubu 400 na sabbin kamuwa da cutar a rana guda.


 

News Source:  DW (dw.com)