ECOWAS ta tsoma baki a rikici Senegal

ECOWAS ta tsoma baki a rikici Senegal
Kungiyar habbaka tattalin arzikin asashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO ta bukaci kai zuciya nesa tsakanin bangarorin da ke kafsawa da juna a kasar Senegal.

Kiran ya zo ne bayan kwashe kwanaki hudu ana bata kashi tsakanin magoya bayan jagoran adawar kasar Ousmane Sonko da jami'an yan sanda.

Fadan dai ya barke tun a ranar Larabar da ta gabata bayan kame jagoran adawar da jami'an tsaro suka yi wanda ya yi sanadiyar ajalin mutun hudu kawo yanzu. 

ECOWAS din ta yi kira ga hukumomin Senegal da su dauki matakan da suka dace domin kawo karshen tashin tashinar.

News Source:  DW (dw.com)