EU ta nuna jimami kan kisan Faransa

EU ta nuna jimami kan kisan Faransa
Shugabar hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta nuna alhini ga al'ummar Faransa bisa fille kan wani dan kasar kuma malamin makaranta.

Ursula Von der Leyen ta ce ta kadu da jin labarin yadda aka kashe malamin makarantar tana mai mika ta'aziyarta ga al'ummar Faransa da suka kasance cikin wannan mawuyacin hali tare da nuna goyon bayanta ga daukacin malaman kasar da na nahiyar Turai.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter shugabar ta kuma kara da cewa idan ba don malaman makaranta ba da babu dimukuradiyya babu 'yancin 'yan kasa. Tuni dai hukumomi suka kama mutum biyar ya zuwa yanzu masu alaka da matashin mai shekaru 18 da yayi kisan a yayin da suka fara gudanar da bincike.

News Source:  DW (dw.com)