Fargabar barkewar fitina a zaben Côte d'Ivoire

Fargabar barkewar fitina a zaben Côte d'Ivoire

Wasu 'yan bindiga sun buda wuta kan ayarin daraktan yakin neman zaben shugaba Alassane Ouattara Patrick Achi, a yayin da ake kasa ga sa'o'i 48 da a gudanar da zaben shugaban kasa mai cike da cece-kuce.

Lamarin ya faru ne a kusa da garin Agbaou mai tazarar kilomita 150 da arewacin birnin Abidjan, kana wata majiyar tsaro ta shedawa kamfanin dillancin labaru na AFP da cewa ba wanda ya samu rauni a harin.

Ana dai ci gaba da gudanar da yakin neman zaben kasar a cikin wani yanayi na rudani da fargabar tashe-tashen hankula, inda kawo yanzu mutun 30 suka hallaka tun bayan yunkurin shugaban kasar na zarcewa karo na uku akan madafan iko.

News Source:  DW (dw.com)