Fursunoni sama da 200 sun tsere a Kogi

Fursunoni sama da 200 sun tsere a Kogi
Rahotani sun bayyana cewa an kashe mutane hudu a harin da 'yan bindga suka kai a gidan yarin, sai dai 'yan sanda sun sha alwashin bin sawun wadan da suka tsere.

Rahotanni daga jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, na cewa wasu 'yan bindiga sun fasa wani gidan yari da ke karamar hukumar Kabba/Bunu tare da kubutar da fursunoni 240.

Hukumomin jihar sun ce akwai mutane 290 da ke tsare a gidan yarin ciki har da wasu 224 da ke jiran shari'a lokacin da maharan suka kai hari da manyan makamai a daren ranar Lahadi.

Kawo yanzu dai ba a tabbatar da maharan ba, sai dai jami'ai sun ce za a ci gaba da farautar fursunonin da suka tsere da kuma maharan da suka kai harin. Fasa gidan yari dai ba sabon labari ba ne a Najeriya, inda yankunan kasar da dama ke fuskantar hare-haren 'yan bindiga. Ko a watan Afrilu, 'yan bindiga sun kai hari hedkwatar ' yan sandan Owerri, inda suka saki fursunoni sama da 1,800.

News Source:  DW (dw.com)