Gbagbo na shirin komawa Cote d'ivoire

Gbagbo na shirin komawa Cote d'ivoire
Na hannun daman tsohon shugaba Laurent Gbagbo na Cote d'ivoire, Charles Ble Goude ya ce yana kan hanyar komawa gida tare da tsohon shugaban kasar ta yankin yammacin Afirka.

Charles Ble Goudemai shekaru 48 kuma tsohon shugaban matasa 'yan fafatuka na Cote d'ivoire, ya tsere daga kasar ne bayan barkewar rikicin siyasar da ya tilasta Gbagbo sauka daga mulki biyo bayan faduwarsa zabe shekaru 10 da suka gabata.

A watan Janairun 2019 ne dai kotun kasa da kasa mai shari'ar masu aikata miyagun laifuka ta ICC da ke birnin Hague a kasar Netherlands, ta wanke mutanen biyu daga zargin aikata laifukan cin zarafin bil'adama, har sai an daukaka kara a kansu.

Laurent Gbagbo mai shekaru 75 da haihuwa dai na birnin Brussels na kasar Beljium, kafin yanke hukuncin na ICC, wanda a yanzu ya samu takardun Fasfo na diplomasiyya kuma ke fatan komawa kasarsa ta haihuwa cikin wannan wata na Disamba.

 

News Source:  DW (dw.com)