Girgizarar kasa ta afka wa Indonisiya

Girgizarar kasa ta afka wa Indonisiya
Wata girgizarar kasa mai karfin gaske ta fada wa gabashi kasar Indonesiya a ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce lamarin ya girgiza mutanen yankin, inda jama'a ta yi ta neman yadda za ta tsira. Sai dai kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ce kawo yanzu bai samu rahotannin asarar rayuka da yawan mutane da suka jikkata ba. Girgizarar kasar mai karfin maki 6.7 a ma'aunin Richta, ta afka wa tsawon kilomita 107 na yankunan da lamarin ya faru. To amma hukumomi sun ce lamarin bai yi kama da wadda za a kira annobar tsunami ba.Kasar Indonesiya mai yawan tsibiri ta shafa fuskantar girgizarar kasa, galibi ana alakanta hakan da yawaitar tsaunuka da kusancita da tekun Pacific. 

News Source:  www.dw.com