Guterres: zan nemi wa'adi na biyu a MDD

Guterres: zan nemi wa'adi na biyu a MDD
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya bayyana a hukumance cewa zai nemi wa'adin jagorancin wasu shekaru biyar bayan wa'adinsa ya kare a watan Disamban wannan shekara.

,Antonio Guterres ya ce yana son wani dama na cimma buri da manufar hukumar bisa tayin da shugaban hukuiar ya masa na neman tazarce. A watan Oktoban 2016 ne Guterres da ke zama tsohon firaiministan Portugal ya gaji tsohon sakatare janar na MDD Ban Ki-moon da kuri'u 193. Ya kuma yi alkawarin dabbaka sabuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasahen duniya tare da tabbatar da zaman lafiya. 

Sai dai tsawon shekaru da hawa kujerar, hukumar ta fuskanci kalubalen yaki da annobar corona da yake yake tare da matsin tattalin arziki da kuma tabbatar da daidaito da warware rikicin kasuwanci tsakanin Amirka da Chaina.

News Source:  DW (dw.com)