Hari ya halaka jami'an tsaron Sudan biyar

Hari ya halaka jami'an tsaron Sudan biyar
Jami'an tsaron Sudan biyar sun halaka kana wasu da dama sun jikata sakamakon harin kwanton bauna a yankin Darfur mai fama da tashe-tashen hankula.

An halaka jami'an tsaron Sudan biyar sakamakon harin kwanton bauna a ynakin Darfur na yammacin kasar, inda 'yan sanda ke zargin tsageru dauke da makamai da aikata kisan.

Hukumomin sun ce akwai kuma wasu jami'an tsaron da suka samu raunika sakamkon wannan hari.

Ita dai kasar ta Sudan ta kasance cikin tashe-tashen hankula tun lokacin da sojoji suka kwace madafun ikon kasar a watan Oktoba na shekarar da ta gabata, inda Janar Abdel Fattah al-Burhan ya dauki madafun ikon kasar.

 

News Source:  DW (dw.com)