Harin kwanton bauna kan gwamnan Borno

Harin kwanton bauna kan gwamnan Borno
Mayakan Boko Haram da ke da alaka da Kungiyar ISIS sun kai sabon harin kwanton Bauna wa ayarin motocin Farfesa Babagana Umara Zulum tare da kashe mutum takwas.


Mayakan Boko Haram da ke da alaka da Kungiyar ISIS sun sake kai wani harin kwanton Bauna wa ayarin motocin gwamman Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, inda su ka hallaka Sojoji 7 da dan Civilan JTF guda daya a kan hanyar zuwa Baga.

Shaidun gani da ido da wasu majiyoyin na jami'an tsaro sun tabbatar da cewa, mayakan na ISWAP sun bude wuta da bindigogi gami da rokoki kan ayarin motocin gwamnan a kan hanyar su ta zuwa duba ‘yan gudun hijira da su ka fara komawa Baga.

Sai dai babu abinda ya samu gwamnan saboda ba ya cikin ayarin yayin wannan hari.

Al'ummar Bornon dai na ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar hare-hare kan gwamna Zulum a daidai lokacin da ya ke neman mafita kan matsalolin tsaron jihar.
 


 

 

 

News Source:  DW (dw.com)