Human Rights Watch ta zargi jami'an Najeriya

Human Rights Watch ta zargi jami'an Najeriya
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch, ta zargi hukumomin tsaro a Najeriya da wuce makadi da rawa musamman kan masu zanga-zangar lumana a kasar.

A ranar Alhamis ta makon jiya ce dai wasu bangarorin matasa a Najeriyar suka fara wani gangamin kin jinin wani bangare na rundunar 'yan sandan kasar da ke yaki da fashi da mamaki wato SARS, abin da ya kai hukumomi rusa rundunar.

Sai dai zanga-zangar ta ci gaba har i zuwa halin da ake ciki, inda wasu ke danganta ta da siyasa  ko ma turje wa gwamnati baki daya.

Ita dai kungiyar ta Human Rights Watch, ta ce martanin jami'an tsaro kan masu zanga-zangar, ya kai ga kisan akalla mutum hudu tare da jikkata wasu da dama.

Wani faifan bidiyo da ya nuno yadda jam'in rundunar SARS da aka rusa suka harbe wani matashi a jihar Delta da ke kudancin Najeriyar a farkon wannan watan ne dai ya haifar da zafin zanga-zangar da ake gani a yau.

News Source:  DW (dw.com)