Jam'iyyar Putin na gab da lashe zabe a Rasha

Jam'iyyar Putin na gab da lashe zabe a Rasha
Zaben na Rasha dai ya gudana yayin da wasu ke kokawa da matsa wa masu sukar lamirin gwamnati lamba, musamman ma hana su zabe da mahukunta suka yi.

Aski ya zo gaban goshi dangane da zaben kasa da ake yi a Rasha a rana ta uku kuma ta karshe da ake zaben 'yan majalisar dokokin kasar.

Jam'iyyar United Russia ta Shugaba Vladimir Putin ce hasashe ke nuna cewa za ta sake dawo da rinjayenta a majalisar.

Zaben na Rasha dai na gudana inda wasu ke kokawa da matsa wa masu sukar lamirin shugaban kasar lamba, musamman ma hana su zabe da mahukunta suka yi.

Kafin fara zaben a ranar Juma'a dai, sai dai aka garkame masu goyon bayan madugun adawar kasar Alexie Navaly, wanda shi ma ke tsare tun cikin watan Janairun bana.

News Source:  DW (dw.com)