
Daukar matakin ya zo ne bayan samun barkewar annobar cutar corona a wata mayanka inda ma'aikata sama da 1500 suka kamu da cutar.
Gwamnan jihar North Rhine-Westphalia da gundumar ta Gütersloh ke cikinta Armin Laschet ya ce sauran jihohi da suka hada da Thuringia da Lower Saxony da sauran wurare a jihar North Rhine-Westphalia sun dauki matakin rufe daukacin gundumar Gütersloh.
Makasudin hakan shine domin shawo kan sake barkewar annobar corona a yankin da kuma gudanar da gwaji domin tantance yaduwar cutar.