Jamus na fuskantar kamarin corona

Jamus na fuskantar kamarin corona
Adadin wadanda suka kamu da annobar corona a Jamus na ci gaba da karuwa, cibiyar yaki da cutattuka masu yaduwa Robert Koch ta ce an samu mutane 7 830 da suka kamu da corona a cikin sa'o'i 24.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga 'yan kasar da su bayar da hadin kai da gaggawa domin ganin an dakile yaduwar cutar.

Da take magana a sakonta na mako mako, Merkel ta ce yana da kyau a dauki duk wasu muhimman matakan da suka dace wajen kawar da yaduwar cutar, kana ta bukaci takaita haduwar jama'a da dage duk wasu tafiye-tafiyen da basa da muhimmanci, tana mai cewa yanzu Jamus na cikin wani yanayi mai sarkakiya.

News Source:  DW (dw.com)