Jamus: Za a fara allurar karin garkuwar jiki

Jamus: Za a fara allurar karin garkuwar jiki
A Jamus za ta fara yiwa al'umma allurar karin garkuwar jiki saboda corona.

Gwamnatin Jamus ta sanar da cewa za ta fara yiwa 'yan kasar allurar bunkasa garkuwar jiki daga watan Satumba mai zuwa tare kuma da saukaka yi wa yara matasa 'yan shekaru goma sha biyu zuwa sha bakwai rigakafin corona.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta sanar da hakan yayin da ake nuna fargaba kan yaduwar kwayar cutar Delta ta Corona.

Ministan lafiya na tarayya Jens Spahn da kwamishinonin lafiya na jihohi 16 na tarayyar Jamus sun cimma matsaya cewa za a fara yin allurar karin garkuwar jikin ga tsofaffi da kuma mutanen da ke fama da wasu cutattuka masu hadari.

Za a tura tawagar jami'an lafiya na tafi da gidanka da za su yi allurar zuwa gidajen kula da tsofaffi da gidajen rainon yara domin yin rigakafin ta allurar Pfizer/BioNTech ko kuma Moderna.

News Source:  DW (dw.com)