Jamus za ta kara wa'adin dokar kulle a kasar

Jamus za ta kara wa'adin dokar kulle a kasar
Shugabar gwamnatin Jamus gami da gwamnonin kasar goma sha shida za su duba yiyyuwar kara wa'adin kulle.

Gwamnatin Jamus na shirin tsawaita wa'adin dokar kulle, bayan da tuni wasu jihohin kasar guda biyu suka nuna cikakken goyon bayansu bisa wannan yunkuri. 

A gobe Talata ne Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel za ta gana da gwamnonin jihohi goma sha shida na kasar, inda za su tattauna tare da daukar mataki na gaba yayin da ake dab da kammala wa'adin dokar kullen da kasar ta shiga a ranar 16 ga watan Disambar bara.

Kimanin makwanni uku ne na dokar kullen ake sa ran karawa, wanda zai kai har 31 ga wannan watan Janairun da muke ciki. Jamus dai na cikin kasashen Turai da aka samu sassaucin annobar.
 

News Source:  DW (dw.com)