Jana'izar Jose Eduardo dos Santos

Jana'izar Jose Eduardo dos Santos
Wasu daga cikin shugabanin kasashen Afirka sun isa birnin Luanda don yi wa tsohon shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos bankwanan karshe.

Shugabanin kasashen Afirka da dama ne ke halatar jana'izar tsohon shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos. An shirya yi wa marigayin da ya kwashi kusan shekaru arba'in kan madafun ikon kasar, faretin ban girma a yayin jana'izar da ke gudana a wannan Lahadin.

A watan Yulin da ya gabata, Dos Santos ya mutu bayan ya sha fama da rashin lafiya a wani asibiti da ke birnin Barcelona na kasar Spaniya da ke yankin Turai. Yan Angola na yi wa Dos Santos bankwanan karshe, mako guda bayan da suka sake zaben shugaba mai ci Joao Lourenco na jam'iyyarsa ta MPLA da ta shafe kusan shekaru hamsin tana mulkin kasar ta Angola.
 

News Source:  DW (dw.com)