Kalubale tattare da zaben Edo

Kalubale tattare da zaben Edo
Har yanzu ana ci gaba da gudanar da zaben kujerar gwaman jihar Edo da ake duk da matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu yankunan da kuma jinkira da aka samu na fara tantance masu zabe saboda matsalar na'ura.

Gwamnan jahar da ke cikin jerin 'yan takara karkashin inuwar jamiyyar PDP, Chief Godwin Obaseki, ya koka cewar Jami'an tsaro na nuna musu rashin adalci yayin wannan zabe da ke gudana zaben musamman kan musgunawar da ya ce ana yi wa kusoshin jamiyyar sa ta PDP da suka ziyarci jahar don duba yadda zaben zai gudana, kamar yadda suma takwarorinsu na jam'iyyar APC suka yi. Wannan ne karon farko da ake gudanar d zabe a kasar Najeriya tun bayan bullar annobar corona da ta haddasa hasarar rayukan jama'a.

News Source:  DW (dw.com)