Koriya ta Arewa: Matakan rage rikici

Koriya ta Arewa: Matakan rage rikici
Koriya ta Arewa ta yanke shawarar dakatar da duk wani shiri da take da shi na daukar matakan soja a kan makwabciyarta Koriya ta Kudu.

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Koriya ta Arewa KCNA ne ya bayyana hakan, inda a hannu guda kuma rahotanni ke nuni da cewa sojojin Koriya ta Arewan sun fara sauke na'urorin amsa kuwwa da suka sake sanyawa a kan iyakar kasar da abokiyar tagwaitakar tata Koriya ta Kudu.

Takaddamar siyasa ta kara kamari tsakanin kasashen biyu tagwaye kana abokan gabar juna, bayan da Pyongyang ta zargi wasu 'yan aware da tura sakon farfaganda cikin kasarta daga Koriya ta Kudun.

News Source:  www.dw.com