Kotu ta tura 'yar adawa gidan yari a Kamaru

Kotu ta tura 'yar adawa gidan yari a Kamaru
Wata kotun soja ta musamman a Kamaru ta tura jagorar mata 'yan adawa  Fri Awasum Mispa zuwa zaman gidan kaso na watanni shida bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati da ta gudanar.

Mispa dai ta kasance jagora a bangaren mata na jam'iyyar MRC ta Maurice Kamto mai adawa da gwamnatin Shugaba Paul Biya. Hukuncin da aka yanke mata ya biyo bayan wata zanga-zanga da ta jagoranta a karshen makon da ya gabata a birnin Yaounde domin nuna adawa da daurin-talalar da gwamnati ta yi wa Maurice Kamto a gidansa.

Sai dai kotun sojin ta ce ta kama wannan mace 'yar adawa da yunkurin kitsa juyin juya hali, a don haka ta tura ta zaman kaso na watanni shida, za kuma a ci gaba da bincike.

News Source:  DW (dw.com)