Madugun adawar Rasha zai koma gida

Madugun adawar Rasha zai koma gida
Jagoran adawar Rasha, Alexei Navalny, wanda ya dora alhakin sanya masa guba a kan fadar Kremlin ta Rashar, na shirin komawa Mosko babban birnin kasar a ranar Lahadin da ke tafe.

Shi dai Mr. Alexei Navalny, wanda kwararrun likitocin Jamus suka tabbatar an sanya masa guba sanfurin Novichok, ya kansace a Jamus din ne tun cikin watan Agustan bara, inda ake yi masa magani.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, babban dan adawar ta Rasha, ya ce sam-sam bai taba tunanin zama a wajen kasar tasa bisa radin kansa ba.

Lamarin na Mr. Navalny ya sanya kungiyar Tarayyar Turai wato EU, kakaba wa kasar ta Rasha takunkumai.

Mutumin dai ya zargi hukumar leken asirin Rashar da sanya masa gubar.

News Source:  DW (dw.com)