Majalisar a Amirka ta cigaba da zamanta

Majalisar a Amirka ta cigaba da zamanta
Hadin gwuiwar majalisar dokokin Amirka ya ci gaba da zaman shi, bayan da magoya bayan Donald Trump suka afkawa ginin majalisar kasar.

Majalisar Dinkin Duniya gami da kasashe masu fada a ji a fadin duniya da suka hada da China da Jamus, sun bayyana abin da ya faru na afkawa harabar majalisar dokokin Amirka da wasu magoya bayan shugaba Donald Trump suka yi a matsayin karan tsaye ga demokaradiyya.

A kalla mutane hudu ne suka rasa rayukkansu cikinsu har da wata mata, inda kuma 'yan sanda suka chafke masu zanga-zanga sama da hamsin a arangamar da suka yi.

Kawo yanzu abubuwa sun fara daidaita a majalisar, kuma gaba kadan za a cigaba da shirin na tabbatarwa zababben shugaban kasar Joe Biden nasararsa. 

News Source:  DW (dw.com)