Matakan tsaro bayan harin ta'addanci

Matakan tsaro bayan harin ta'addanci
Hukumomi a Faransa sun kara tsarurara matakan tsaro a ko ina cikin fadin kasar biyo bayan wani harin ta'addancin da ya hallaka mutun uku a majami'ar Nice da ke kudancin kasar.

Shugaba Emmaneul Macron ya bayyana kara adadin jami'an tsaron da za su yi sintiri domin tabbatar da tsaro da doka da oda, kana kuma nan gaba a yau a ke sa ran majalisar tsaron kasar zata gudanar da wani zamanta na musaman kan batun,

Kasashe da dama na duniya na ci gaba da nuna alhini da ma yin kakkausar suka kan harin ta'addancin ciki har da na nahiyar Turai da Amirka, inda Shugaba Donald Trump yayi Allah wadarai da abinda ya kira hari kan abukiyar dasawar Amirka wato Faransa.

Su ma dai wasu kasashen Musulmai irin su Turkiya da Saudiya da Iran sun soki harin, a yayin da Tunisya da ake zargin wanda ya kaddamar da harin dan kasar ta ne ta bayya anniyarta na kaddamar da bincike.

News Source:  DW (dw.com)