Matsin lamba kan sace yara a Najeriya

Matsin lamba kan sace yara a Najeriya
Bukatar ceto yaran maza da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su na kara yaduwa a Najeriya, inda jama'a ke amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen kira ga gwamnatin tarayya.

Korafe-korafen ganin an ceto yara 'yan makarantar sekandare da aka sace tare da yin garkuwa da su na kara zafafa a kafofin sadarwa na zamani a Tarayyar Najeriya. A daren ranar Jumma'ar da ta gabata ne wasu gungun 'yan bindiga suka yi dirar mikiya a wata makarantar sekandare ta maza da ke karamar hukumar Kankara a jihar katsina a yankin Arewa maso yammacin kasar, inda suka yi awon gaba da yara kusan 600.

Wata majiya ta ce cikin yara sama da 800 'yan makarantar, 200 ne kachal suka samu damar kubuta daga komar 'yan bindigar. Lakabin "BringBackOurBoys" wanda ke kira da a ceto mana yaranmu shi ne dai ya karade kafofin sadarwar kasar a ranar Lahadin nan.

News Source:  DW (dw.com)