MDD: "A daina zargin 'yan agaji a Tigray"

MDD: "A daina zargin 'yan agaji a Tigray"
Mataimakin Sakatare Janar na MDD mai kula da ayyukan jin kai Martin Griffiths ya yi tir da zargin da gwamnatin Habasha ke yi wa ma'aikatan agaji a yankin Tigray duk da matsalar da suke fuskanta wajen jigilar abinci.

A baya dai fadar mukkin ta Adis-Ababa ta zargi ma'aikatan agaji da hada kai da dakarun kungiyar TPLF tare da samar musu da makamai. Sai dai a  yayin wani taron manaima labarai  da ya gudanar a babban birnin Ethiopiya, sabon mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai, Martin Griffiths ya ce: dole ne "zargin da ake yadawa kan ma'aikatan agaji a daina, domin ba su da tushe da makama."

 Akalla ma'aikatan agaji 12 ne aka kashe tun lokacin da Firayimnistan EThiopiya Abiy Ahmed ya tura sojojin gwamnatin zuwa Tigray don korar hukumomin yankin daga madafun iko kusan watanni tara da suka gabata. Sai dai tun watan Yuli, fada ya bazu zuwa yankin Afar da kuma yankin Amhara, wadanda ke da iyaka da Tigray.

    

 

News Source:  DW (dw.com)