MDD ta yi tir da kisan dalibai a Kamaru

MDD ta yi tir da kisan dalibai a Kamaru
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rashin jin dadinta da wani sabon harin da wasu suka kai kan dalibai da ke karatu a wata makaranta da ke yankin Kamaru renon Ingila.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kaduwa da wani sabon harin da aka kai kan daliban wata makaranta da ke yankin kasar Kamaru mai amfani da Ingilishi, inda sabbin alkaluma ke cewa mutum takwas ne suka salwanta.

Maharan dauke da bindigogi da kuma adduna sun far wa yaran ne a yankin Kumba a jiya Asabar, yankin da rikici ke ci tsakanin 'yan aware da dakarun gwamnati shekaru uku ke nan.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka Moussa Faki Mahamat, ya ce babu kalaman da za a iya amfani da su wajen bayyana rashin dacewar abinda wadannan mahara suka aikata kan yara.

Shi ma ministan lafiya a Kamarun, Malachie Manaouda, ya yi Allah wadai da lamarin da ya ce ba shi da wata ma'ana.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kisan wadannan daliban na yankin kudu maso yammacin kasar ta Kamaru.

News Source:  DW (dw.com)