Mutum na karshe na harin Kanada ya mutu

Mutum na biyu kuma na karshe da ake zargi da kai harin da ya halaka mutane 10 a Kanada ya mutu bayan 'yan sanda sun kama shi, sakamakon raunika da ake kyautata zaton ya yi wa kansa.

Mutum na biyu da ake nema a kasar Kanada kan kisan mutane 10 da wuka, ya lardin Saskatchewan, shi ma ya mutu. Dan shekaru 30 da haihuwa tun farko 'yan sanda sun kama shi kusa da garin Rosthern.

An kai shi asibiti inda aka tabbatar da ya mutu. An zargi shi ya ji wa kansa rauni. Lokacin harin na maharan biyu 'yan uan juna da yanzu duk sun mutun, sun halaka mutane 10 tare da jikata wasu kusan 20.

Tuni mahukuntan Kanada suka kaddamar da bincike domin sanin hakikanin abin da ya faru game da harin. Lamarin ya kasance mafi muni a tahirin kasar ta Kanada cikin 'yan shekarun da suka gabata.

 

News Source:  DW (dw.com)