Najeriya: Ma'aikatan wutar lantarki sun shiga yajin aiki

Najeriya: Ma'aikatan wutar lantarki sun shiga yajin aiki
Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya ta tsunduma yajin aikin gama gari wanda ya jefa birnin Abuja hedikwatar Najeriyar da mafi yawan sassan kasar cikin mumunan hali na rashin wuta lantarki.

Kungiyar ma’aikatan ta na yajin aikin ne kan wasu korafe-korafe da suka hada da batun karin girma na kanana da manyan ma’aikata da kuma wasu ma’aikansu da aka sallama daga aiki 

Muazu Ibrahim sakataren kungiyar ma’aikatan wutar lantarkin ya shaida wa wakilinmu da ke Abuja Uwaisu Abubakar Idris cewa ma’aikatan wutar lantarkin sun kashe dukkanin naurorin wuta lantarki a sassan kasar.


 

News Source:  DW (dw.com)