Nasara kan 'yan Boko Haram

Nasara kan 'yan Boko Haram
Shugaba Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar ya jinjinawa dakarun sojan kasar kan abinda ya kira namijin kokarin da suka yi wajen karya lagon mayakan Boko Haram a Diffa.

A yayin wata ziyarar aikin da ya ke ta tsawon kwanaki biyu a yankin Diffa na Kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar, Shugaba Bazoum ya ce ya gamsu matuka da ganin irin ci gaba da aka samu ta fannin tattabatar da tsaro, kana kuma hakan na nuni da cewa karara askarawan kasar sun kama hanyar lashe yaki da 'yan ta'adda na Boko Haram.

Sai dai a yayin da yake jawabi a gaban wata bataliyar askarawan kasar a Geskerou mai iyaka da Najeiya, Mohamed Bazoum ya kara da cewa yana da kyau sojan kasar da su kara daura damara domin har yanzu akwai birbishin rina a kaba.

Hukumomin yankin dai sun ce kimanin yan gudun hijirar da suka baro gijensu fiye da dubu 26 ne suka koma kauyukansu, bayan kaddamar da wani shirin gwamnatin kasar na sake tsugunar da su a gidajensu na asali.

News Source:  DW (dw.com)