Qatar ta yi wata ganawa da Taliban

Qatar ta yi wata ganawa da Taliban
Ministan harkokin wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani ya kai ziyara Afganistan don ganawa da Firanminstan gwamnatin Taliban Mullah Muhammad Hassan Akhund.

Abdulrahman Al-Thani dai shi ne babban jami'in gwamnati na farko da ya kai ziyara kasar tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace ikon Afganistan a watan Augustan shekarar 2021. 

A sakon da Taliban din ta wallafa a Twitter, ta ce ministan ya kuma gana da manyan jami'an gwamnatinta, ko da yake ba a baiyana jigon tattaunawarsu ba.

Kasar Qatar dai ta dade ta na aikin shiga tsakani kan Afganistan, inda ta jagoranci tattaunawa tsakanin kungiyar da kasar Amirka a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Donald Trump da kuma hambararren shugaban kasar Afganistan Ashraf Ghani.

News Source:  DW (dw.com)