Rasha ta daure 'yar wasan Amirka kan laifin maye

Rasha ta daure 'yar wasan Amirka kan laifin maye
Wata kotun Rasha ta yanke wa fitacciyar 'yar wasan kwallon kwando na Amirka Brittney Griner hukuncin daurin shekaru Tara a gidan yari, kan mallakar kwayoyin maye da safararsu.

A watan Yuli na shekarar  Griner mai shekaru 31, ta amsa laifinta a gaba kotu tare da cewa ba da gangan ta mallaki abubuwand a ake zarginta ba, yanzu haka dai kotun ta ci tarar 'yar wasan da ta zama zakaran Olympics na Amirka har sau biyu a kwallon kwando tarar kudi dala dubu 16 da 700.

Sai dai Shugaban Amirka Joe Biden ya yi tir da hukuncin kotun, hukuncin kotun na zuwa ne a dai-dai lokacin da dangantaka ke kara tsami tsakanin Amirka da Rasha kan yakin Ukraine.

News Source:  DW (dw.com)